Tsaro

Ba daidai bane Gwamnati taci gaba da dawainiya da tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram alhali har yanzu kasarnan tana fama da ayyukan ta’addancin kungiyar, In ji Sanata Ndume.

Spread the love

Ali Ndume, Sanata mai wakiltar Borno-ta Kudu ya yi Allah wadai da shirin gwamnati na gyaran tsofaffin mambobin kungiyar Boko Haram.

Sanatan wanda ya yi ta fadin albarkacin bakinsa game da rashin dacewar shirin ya sake nuna bacin ransa yayin da yake magana a wani taron kasafin kudi da sojojin Najeriya a ranar Laraba.

Ya ce ba daidai ba ne a ci gaba da gyara tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram alhali har yanzu kasar na fama da ayyukan ta’addancin kungiyar.

Ndume ya ce: “Ina cikin rashin jituwa da gwamnati.”

Ya yi nuni da cewa wasu tubabbun ‘yan Boko Haram suna kutsawa cikin al’umma ne kawai don tattara bayanan sirri da shirya hare-hare a kan al’umma.

Ya ambaci harin Damboa na baya-bayan nan inda wani, “wanda ya tuba dan Boko-Haram yana turawa da kungiyar ta’adda bayanai game da motsin sojoji”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button