Siyasa

Ba Karamin Rashin Dabara Bace, Ba Karamin Rashin Hikima Bace Kama Ashir Sharif~Bashir Tofa.

Spread the love

Bashir Tofa Ya Gargadi Buhari Kan Kama Masu Zanga-zanga.

Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Fitaccen dan siyasar nan wanda ya tsaya takara a zaben 1993, Alhaji Bashir Tofa ya umarci shugaba da ya sa a saki shugaban kungiyoyin da suka yi zanga-zanga kan tabar-barewar tsaro a Arewa kafin matasa su hasala su soma tayar da hankali.

A sakon da ya fitar jiya Laraba, tsohon dan siyasar ya yi kira ga shugaba Buhari da Babban Sufeton ‘yan sanda da shugaban hukumar DSS suy gaggauta sakin [Nastura] domin idan samarin nan suka kufula suka fara barna a kasar nan, wallahi ba a san inda za ta tsaya ba.

Alhaji Bashir Tofa ya kara da cewa ba karamin rashin dabara ba ce, ba karamin rashin hikima ba ce kama Nastura Ashir Sharif ganin cewa babu wanda ya tayar da hankali lokacin zanga-zangar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button