Ba kudi muke bukata ba, budurcinta muke so – Masu garkuwa da mutane ga mahaifin budurwa.
Daga:- Jamil Usman
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun sace wata budurwa mai suna Patience Emmanuel mai shekaru 20 da ke karatu a jami’ar jihar Bauchi. Bayan nan, sun sanar da mahaifinta cewa basu bukatar kudi, budurcinta kadai suke bukata.
A yayin bayyanawa manema labarai halin da yake ciki, Emmanuel Kushi, wanda ma’aikacin gwamnati ne, ya sanar da cewa diyarsa ta je gidan dan uwanta da ke Rafin Zurfi a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni da niyyar dauko wani abu.
Amma kuma bata isa gidan ba kuma ba a samunta ko a waya, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
Zuwa da yamma, dan uwanta ya dinga kiranta amma ba a dauka. Daga bisani kuwa ba a samun wayar kwata-kwata.
Kushi ya bayyana cewa, “washegari na tura sakon karta kwana zuwa wayar diyata amma amsar da na samu ta bani mamaki.”
“Kana tunanin za ka sake ganinta ne nan gaba? Wawa,” aka bada amsa.
Ba kudi muke bukata ba, budurcinta muke so – Masu garkuwa da mutane ga mahaifin budurwa. Hoto daga shafin Linda Ikeji.
Kushi ya ce ya tafi gonarsa inda ya sake samun sako daga wadanda suka sace diyarsa. “Baba, diyarka na tare da mu. Bamu bukatar kudi, budurcinta kawai muke bukata. Kada ka nemeta.”
Rikitaccen mahaifin ya ce yana kokarin gane sakon da aka turo masa amma sam bai yarda da ikirarinsu ba.
“Wurin karfe 10:25 na safe, an turomin wani sako inda aka ce min ta mutu. Muna ta kokarin samunta amma har yanzu shiru. Abu daya da na sani shine diyata na nan da ranta. Na yi imanin za ta dawo da ranta,” Kushi yace.
Kushi ya ce shi da iyalansa sun fada addu’a ba dare ba rana don ganin dawowarta cike da koshin lafiya.
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmed Wakil, ya ce a halin yanzu ‘yan sanda na bincikar al’amarin kuma za su bankado masu hannu a ciki.
A wani labari na daban, korarren dan sandan da ya kware a satar babura ya shiga hannun jami’an tsaro a jihar Bauchi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta damke wani korarren dan sanda mai mukamin sajan mai suna Makama Musa mai shekaru 34, bayan aikata fashi da makami da yayi.