Ba Kunya Ba Tsoran Allah Sun Rungume Juna A Bainar Jama’a.
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.
Duk da ban so yin rubutu akan abin da ya faru ba, amma kuma ya zama wajibi agareni in yi bulaliya akai, wala Allah ko a sami gyara.
Lokacin da na kalli bidiyon saurayi da budurwar da suka rungumi juna saboda anyi musu baiko abin kunya yabani, duk da ba nine na aikata hakan ba amma sai nakasance ina jin kunya sakamakon aukuwa lamarin.
Wai ace Mutum Bahaushe Dan Arewa Kuma Musulmi Dan Musulmi Jikan Musulmi Ya Rungume Mace Bahaushiya Kuma Musulma ‘Yar Musulmai A Bainar Jama’a, da alama ma agaban danginta da danginsa hakan tafaru, basuji kunyar jama’a ba, ka ga ko ba za ayi maganar tsoron Allah ba
Idan muka ajiye batun addini ko a al’darmu ta Hausawa ma hakan abin kunya ne, kuma abin Allah wadai ne.
A addinance ko ba ma sai na fada muku ba, kowa ya san haramun ne ka taba wadda ba muharramarka ba, balle ma har ka rungumeta.
Gyara Kayanka Ba Zai Zama Sauke Muraba Ba.