Rahotanni

Ba makarantar Abduljabbar Nasiru kabara muka rushe ba, filin gwamnatin kano ne__in ji kwaminishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba.

Spread the love

Kwamishinan yaɗa Labarai na jihar Kano ya ce ba makarantar Abduljabbar Nasiru Kabara ta rushe ba filin gwamnatin Kano ne a filin mushe da wasu sukai gine gine a ciki gwamnatin kano ta rushe.

Muhammad Garba ya ce daman can gwamnatocin suna da shiri na Gina makaranta a wajen, amma suka Sani dai shine kawai shi Abduljabbar yakanyi taronsa na wa’azi a wajen Wanda har ta sa ya fara gine wasu sassa na filin.

Muhammad Garba ya kara da cewa shi wannan gini da ke filin mushe an dade ana samun rigingimu akansa sakamakon wasu daga cikin darikun da ke jihar kano na ikirarin cewa gwamnati ta mallaka musu shi inda har ta kai ga sun fara assasa gininsu a filin.

Muhammad Garba ya ce yanzu kuma gwamatin kano ta ga ya dace ta tabbatar da wancan kudiri tun na gwamnatocin baya na Gina makaranta a wajen, wannan shine dalilin rushe wannan gini tunda daman mallakin gwamnatin Kano ne babu abin da ya hada Abduljabbar Nasiru Kabara da wannan filin, cewar kwamishinan yada labarai na gwamnatin kano Muhammad Garba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button