Ba ruwa na ko kun zabe ni ko ba Baku zabeni ba zan tabbatar nayi Adalci ga kowa da kowa a jihar Kaduna ~Cewar Uba sani.
Zababben Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya yi alkawarin gudanar da mulkin al’ummar Jihar cikin adalci ba tare da la’akari da ko sun zabe shi ba a zaben da aka kammala ba.
Uba Sani wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa a halin yanzu ya ce Allah madaukakin sarki ne ya kaddara zabensa a matsayin zababben gwamna wanda ke ba da mulki ga wanda yake so.
A cewarsa, “Abu ne kawai ke faruwa a lokacin da Allah Ta’ala ya so ya faru.
“Za mu yi adalci ga kowa kuma za mu jagorance su cikin adalci da da Amana.
“Dukkan masu zabe a Kaduna, ko kun kada kuri’ar ku ko ba ku zabe mu ba, za mu yi wa kowa adalci kuma za mu jagoranci kowa cikin adalci da yardar Allah.
“Kamar yadda ka sani, lokacin da muka yi nasara, abin da ya zo a raina shi ne cewa mulki daga Allah yake, kuma yana ba da shi ga wanda yake so kuma a lokacin da yake so.