Labarai

Ba tare da biyan ku’din Fansa ba Kawo yanzu mun kubtar da mutane sama da mutun dubu daya daga hannun ‘yan ta’adda ~Nuhu Ribadu.

Spread the love

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana a ranar Litinin din da ta gabata cewa, a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu, gwamnatin tarayya ta yi nasarar ceto sama da mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ba.

Ya ce, “A madadin shugaban kasa, ina mika godiyata ga duk wadanda suka yi nasarar ceto wadanda abin ya shafa ba tare da an rasa kowa daga cikinsu ba ko kuma biyan kudin fansa.

“Wannan kuma wani labari ne na nasara a kokarinmu na ‘yantar da duk wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba.

“Ya zuwa yanzu mun saki irin wadannan mutane sama da dubu ba tare da hayaniya ba tare da mutunta sirrinsu da amincin su.

“Wannan taron shine mataki na karshe a cikin jerin ayyukan ceto da muka yi a cikin ‘yan watannin da suka gabata, don ‘yantar da wadanda aka yi garkuwa da su a baya-bayan nan.

“A ci gaba, muna ƙarfafa jami’an tsaro da matakan tsaro don hana waɗannan sace-sacen da kuma karfafa tsaro ta jiki a cikin al’ummomin da ke da rauni a Nageriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button