Ba za a daina kashe ‘yan Arewa ba a karkashin mulkin Buhari__Nastura Ashir sheriff.
Shugaban gamayyar cigaban kungiyoyin Arewa Alhaji Nastura Ashir sheriff ya ce ba za a daina kashe ‘yan Arewa ba a kudancin Najeriya a karkashin mulkin Buhari.
Alhaji Nastura Ashir sheriff ya bayyana cewa wannan wata dama ce ‘yan kudu suka samu har suke kisan kiyashi akan ‘yan Arewa a jihohin su.
Nastura Ashir sheriff ya karaa da cewa saboda imanin da ‘yan kudu suke dashi cewa babu abin da zai faru don sun yi kisan kiyashin kan ‘yan Arewa a karkashin mulkin Buhari.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa Alhaji Nastura Ashir sheriff ya ce saboda tsabar rashin martaba rayukan ‘yan Arewa da gwamnatin Buhari ke yi yajanyo hakan.
Alhaji Nastura ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema Labarai a Kaduna dangane da halin da ‘yan Arewa suka tsinci Kansu Na kisan kiyashin da ake musu yanzu haka a sashin kudancin Najeriya musamman jihohin yarabawa.
Daga Kabiru Ado Muhd.