Labarai

Ba Za Mu Ci Gaba Da Jure Hana Ayyukanmu ba – EFCC

Spread the love

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi gargadi ga jama’a da cewa laifi ne a hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal.

Sashi na 38(2)(a(b) na dokar kafa hukumar EFCC ya sanya laifin hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal. Masu aikata irin wannan laifi na iya fuskantar daurin kurkuku na kasa da shekaru biyar.

Wannan gargadin ya zama dole bisa ga yadda mutane da kungiyoyin da Hukumar ke bincike ke kara ta’azzara daukar doka a hannunsu ta hanyar daukar ‘yan baranda domin dakile ayyukan EFCC.

A lokuta da dama, jami’an Hukumar sun yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan tada zaune tsaye domin gujewa tabarbarewar doka da oda. Abin takaici, ana ɗaukar irin wannan halin a matsayin alamar rauni.

Don haka hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba domin kuwa za a fuskanci hukuncin da ya dace.

Dele Oyewale
Head,  Media & Publicity
April 17, 2024

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button