Labarai

Ba za mu tattauna da ‘yan bindiga ba – Gwamna Lawal ya dage

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jaddada alkawarin gwamnatinsa na cewa ba za ta taba yin sulhu da barayi da ‘yan fashi da makami ba domin samar da zaman lafiya.

Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa Malam Mani Mumuni ya ce gwamnatinsa a shirye take tana maraba da duk wata jam’iyyar adawa a fafutukar kawo karshen rashin tsaro a jihar, inda ya ce shi ba jagoran jam’iyyar PDP kadai ba ne, illa jihar baki daya.

“Ni ba Gwamnan PDP kadai bane, ni ne Gwamnan Zamfara gaba daya, don haka kowa ya cire wariya daga gwamnatina,” ya kara da cewa.

Ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke kan zabensa nasara ce ga dimokradiyya da kuma ci gaban kasa baki daya.

“Ba komai ko wanene APC ko PDP, nine gwamnan jihar Zamfara ba tare da la’akari da jam’iyya ko kabila ba”

Dauda Lawal ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishinsa da ke Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce bangaren shari’a ya tabbatar da amincinsa a matsayin fata na karshe ga talaka, ya kuma yaba musu da hangen nesa.

Mataimakin Gwamnan ya ce gwamnatin a shirye take sosai don kawo karshen rashin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa ba za a amince da duk wani aiki na cin amana ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button