Labarai

Ba za mu yarda da bayar da belin masu garkuwa da mutane ba, in ji Wike

Spread the love

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Ezenwo Nyesom Wike, ya sha alwashin hana bada belin masu garkuwa da mutane.

Hakan na zuwa ne yayin da ya umurci shugabannin kananan hukumomi shida na yankin da su fara tarukan tsaro na wata-wata don inganta harkokin tsaro a yankunansu ko kuma a sanya musu takunkumi.
Ministan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a yayin wani taron tsaro da aka yi a Abuja Municipal Area Council AMAC.

Wike ya ce masu ruwa da tsaki su sanar da shi idan wani daga cikin shugabannin ya kasa gudanar da taron tsaro na wata-wata.

Ya ce duk shugaban karamar hukumar da ba ya gudanar da taron majalisar tsaro na wata-wata ya zama barazana ga tsaron majalisar.

Ministan ya ce; “Lokaci ya wuce da za a ba da belin masu garkuwa da mutane. Ba zan sake yarda ba. Za mu tabbatar an hukunta mai garkuwa da mutane. Ta yaya za a ba da belin mai garkuwa da mutane?

“Saboda haka, zan kira taro na dukkan shugabannin gargajiya, ganawa da shugabannin kansiloli da ganawa da dukkan hukumomin tsaro. “Idan ba a yi wani taro na wata-wata ba ta fuskar tsaro a majalisun, ya kamata in sani, kuma zan dora wa wannan shugaban alhakin duk wani abu na rashin tsaro idan ya faru.

“Idan kun yi aikinku, ni na yi aikina, shugabannin gargajiya na yin nasu, su kuma jami’an tsaro suna aikin nasu, ba za mu samu matsala ba. Amma idan ba ku yi naku bangaren ba, ni ba nawa nake yi ba, shi kuma ba nasa yake yi ba, to lallai muna da matsalar tsaro baba kenan.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button