Labarai

Ba za’a iya magance Matsalar ta’addanci Cikin karamin Lokaci ba a Nageriya ~IBB

Spread the love

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, za a iya magance ta amma tana bukatar shiri na dogon lokaci.

A wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, Janar Babangida ya ce kasar za ta iya shawo kan matsalolin tsaro idan wadanda ke kan mukamai suka shirya yadda ya kamata.

Ya ce kawar da barazanar da masu satar mutane, ‘yan fashi, da masu tayar da kayar baya ke bukatar babban shiri, ya kara da cewa wannan ba wani shiri ba ne na gajeren lokaci.

Janar IBB ya ce ya samu bayanai da ke nuni da cewa hukumomin tsaro na aiki tare don tsara sabbin dabaru kan yadda za a shawo kan lamarin.

Tsohon shugaban kasar yayin bayyana cewa ya damu da halin da kasar ke ciki, ya bukaci gwamnati da ‘yan kasa da su hada karfi don shawo kan matsalar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button