Labarai

Ba zamu binciki su Burtai da Laifin rashawa ba ~Inji Gwamnatin Buhari

Spread the love

Ministan yaɗa labarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed ya ce babu buƙatar gudanar da bincike kan tsoffin manyan hafsoshin tsaro da aka musanya da sabbi a makon da ya gabata.

Ya ce akwai ka’idoji hanyoyin cikin gida da za su magance su.

Babban Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya da wasu ƴan Najeriya sun buƙaci a binciki wasu kwamandojin sojin domin gano halin taɓarɓarewar tsaro a lokacin mulkinsu.

Amma Lai Mohammed ya ce “manyan hafsoshin tsaron sun yi biyayya ga dokokin aiki. Idan akwai inda aka saɓa akwai ka’idoji na cikin gida da ke da alhakin kula da hakan.”

Ya ce “waɗanda ke kira a binciki tsoffin hafsoshin tsaron a kotun ICC ba masu kishin ƙasa ba ne.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button