Rahotanni

Ba Zamu Gajiya Fagen Rokon Allah Yakawo Mana Karshen Covid – 19 Ba — Sanata Shekarau

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

A Dai -Dai Lokacin Da Al’ummar Musulmi ke cigaba Da Gudanar Da Bukukuwan Idin Karamar Sallah a Yau, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai Kan Ayyukan Jinkai, Kuma Dan Majalisar Dattijai Mai Wakiltar Kano Ta Tsakiya, Daga Jam’iyya Mai Mulki Ta APC, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, Ya Roki Al’ummar Musulmin Najeriya Akan Cewar Kada Su Gajiya Fagen Yiwa Kasarnan Addu’o’in ciyar Da ita Gaba, Tare da Rokon Allah Yakawo Karshen Wannan Annoba Ta Covid – 19 Da tayiwa Kasarnan Katutu.

Haka Zalika A Sakon Mai Dauke Da Sa hannun Tsohon Gwamnan Na Jihar Kano, Ya taya Al’ummar Musulmi Murnar Zagayowar Wannan Rana Ta Idin Karamar Sallah, Sannan Ya taya Al’ummar Musulmi Murnar Kammala Azumi 30 Na Watan Ramadan Cikin Koshin Lafiya Da Nisan Kwana,

Duba Da Yanayin Da Ake Ciki Na Kuncin Rayuwa Da Annobar Corona Virus Ta Haifar a Fadin Kasashen Duniya, a Wannan Lokaci Na Gudanar Da Wannan Bukukuwan Karamar Sallah Ta Bana, Sanata Shekarau ya Bukaci Al’ummar Musulmi Dasu Dauki Hakan a Matsayin wata Sadaukarwa Da Mutane Zasuyi Domin Taimakawa Gwamnati Don Ganin An Shawo Kan Annobar Ta Covid – 19 a Kasarnan.

Sannan Munjiyo Sanatan Yana Bayyana cewar ” Bazamu Gajiya Fagen Rokon Allah Kan yakawo Mana Karshen Wannan Annobar Anan Kusa ba”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button