Labarai

Ba zamu iya bawa dukkan makarantu Tsaro ba kawai Ku kula da ‘ya ‘yan ku ~Inji Gwamtin Buhari.

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta jaddada bukatarta ga ‘yan Najeriya su yi taka tsantsan don kawo karshen hare-hare a makarantu da sace daliban
Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The PUNCH a ranar Litinin, ya nuna cewa gwamnati ba za ta iya tabbatar da Tsaro ga kowace makaranta a kasar ba.
A cewarsa, gwamnati ta umarci makarantu su kai rahoton duk wata barazanar tsaro ga hukumar tsaro mafi kusa.

A hirar, an tambayi ministar abin da gwamnati ke yi don kare makarantu daga hare-haren ‘yan fashi.

Ya amsa, Gwamnatin Tarayya ba za ta iya tsare kowane gida ba. Kowa na buƙatar yin taka tsan-tsan. Mun isar da wannan saƙon ga dukkan makarantunmu domin a ko’ina idan akwai wata barazana, sun san hukumar tsaro mafi kusa da za ta tuntuɓi “.

Nwajiuba ya kuma yi ikirarin cewa kusan duk makarantun kasar nan an killace su. “Kusan dukkan makarantun da ke Nijeriya, ko masu zaman kansu ne ko kuma na Gwamnatin Tarayya, galibi dukkansu masu shinge ne, in banda wasu makarantun jihar.

“Kamar yadda kuma ku sani, ko da kun sanya shinge, wadannan mutane (‘yan fashi) an san su da zuwa ta kofofi.

“Don haka, shingen kewayen, ba shi da wani tasiri kawai Ku Sanar da Jami’an tsaro mafi kusan idan Kun samu wata sanarwar barazana Inji Minisatan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button