Labarai

Ba zamu iya dawo da tallafin man fetir ba domin wasu mutane ne ke anfana a maimakon ‘yan Nageriya.

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa, Sen. Kashim Shettima ya koka da cewa wadanda suka yi asara sakamakon cire tallafin, sun kuduri aniyar kawo cikas ga manufofin gwamnati da shirye-shiryen gwamnati.

Ya yi wannan zargin ne a Abuja a wajen taron shekara-shekara na hada-hadar kudi karo na 16 da Cibiyar Ma’aikatan Banki ta Najeriya (CIBN) ta shirya.

Sen. Shettima ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jajirce wajen yanke shawara, manufofinta da shirye-shiryenta, ya kuma sha alwashin cewa ba za a iya dawo da tallafin ba.

Kashim ya zargi masu anfana da tallafin man fetir wasu mutane ne da Basu bayyana fuskarsu wanda yakamata ace Yan Nageriya ne ke anfana ba wai wasu shafaffu da Mai ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button