Uncategorized

Ba Zamu Janye Daga Yajin Aikin Sai Mama Tagani Ba Har Sai Ansamu Dai-Daito Tsakninmu Da Gwamnati. Cewar Malam Jami’oi (ASUU).

Spread the love

Kungiyar ASUU ta magantu kan lamarin janyewa daga yajin aiki.

Kungiyar Malaman jami’o’i ta Najeriya ta yi watsi da jita-jitan da ke yawo a kafofin ra’ayi da sada zumunta cewa mambobinta sun janye daga yajin aikin da suka tafi tun watan Maris.

Kungiyar ta yi tsokacin haka ne ta shafinta na Tuwita yayinda matasa a Tuwita suke gaddama kan janye yajin aikin.

A cewar kungiyar, rahoton karya ne, na bogi ne, kuma babu kamshin gaskiya ciki. “Sabanin rade-radin dake yawo a kafafen ra’ayi da sada zumunta cewa kungiyar Malaman jami’a ASSU sun janye yajin aikin, babu gaskiya cikin haka.”

Idan zamu janye yajin aiki, akwai matakai da ake bi kuma har yanzu bamu bi matakan ba.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemu, ya lashi takobin cewa kungiyar ba zata gushe tana yaji ba har sai gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatunta.

Ogunyemi ya ce ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar 2012 da akayi. Ya kara da cewa abin takaici ne ace tun shekarar 2009 malaman jami’a basu samu sauyin albashi ba. Ya jaddada cewa wajibi ne a duba lamarin kafin ASUU ta janye wannan yajin aikin. A cewarsa, “Ga matsalan albashi, ba’a magance ba.

Da alamun akwai wasu kusoshi a gwamnati da suka rantse sai mambobinmu sun wahala ta hanyar rike musu albashi.

Malaman Jami’a sun shiga yajin aiki gab da bulluwar cutar Korona a wata Maris. Tun daga lokacin daliban jami’o’in gwamnati dake kasar gaba daya suke zaune a gida.

Daga Comr Haidar H Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button