Labarai

Ba zamu saurari malaman dake Cewa kar’ayi mukabala da Sheikh Abdujabbar ba zamu saka Ranar Zaman ~Ganduje

Spread the love

Ana sa ran Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai karbi rahoton kwamitin game da shirin muhawarar da ake shirin yi tsakanin Shiekh AbdulJabbar Nasiru Kabara da malaman na Kano a yau Litinin 22 ga Fabrairu, 2021.

Kwamishinan harkokin addini na jihar, Dakta Tahar Adamu, ya ce jama’a ba su fahimci sanarwar makonni biyu da gwamnatin jihar ta bayar a baya ba, “Sanarwar makonni biyun da gwamnatin ta bayar ita ce kwamitin ya yi aiki a kan shirin tare da gabatar ga gwamna. ”

Ya lura cewa sanarwar da aka fitar a makon da ya gabata ba ta nuna cewa tattaunawar za ta yiwu a yau ba. “Kwamitin ya kammala aikinsa, kuma ya gayyaci duka hukumomin tsaro da malamai daga ciki da wajen jihar. Inji.

Ya kara da cewa Gwamnan zai yi nazarin rahoton da kwamiti ya gabatar masa tare da sanya ranar tattaunawar.

Dr. Adamu ya ce gwamnati ba za ta saurari wadannan malaman ba wadanda ke bayar da fatawar tattaunawar.

Rahotan Sahelian Times

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button