Kungiyoyi

Ba Zamu Zabi Wanda Ya Wuce Shekaru 70 Shugaban Kasa Ba A 2023 Shugaban Kungiyar matasan Arewa.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Shugaban kungiyar matasan Arewa, Yarima Shattima ya bayyana cewa a shekarar 2023 ba zasu zabi mutumin da ya wuce shekaru 70 a matsayin shugaban kasa ba.

Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da Sunnews inda yace yana tare da maganar da dan uwan shugaban kasa, Mamman Daura yayi na cewa cancanta ya kamata a yi ba karba-karba ba. Hutudole ya ruwaito cewa, Shattima yace Tsarin karba-karba be tsinanawa Najeriya komai ba dan haka ba za’a ci gana da yinsa ba.

Yace ko daga ina dan takara yake indai ya cancanta kawai za’a goya masa baya ya tsaya takara ba tare da nhna banbanci ba. Hutudole ya fahimci Shattima ya kuma ce ba zasu yadda wata jam’iyya daga Arewa ta ce musu wai dan wani yanki ne kawai zai tsaya takara ba.

Da aka ce masa shin yana nufin ba zasu yi Atiku a shekarar 2023 ba kenan ganin cewa ya zarta shekaru 70?

Sai yace bai kira sunan kowa ba kuma bai ma san Atiku ko ya zarta wadannan shekaru ba, yayi maganane data shafi kowa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button