Labarai

Ba zan lamunci kisan Gilla kan Al’ummar jihar Kaduna ba ~Gwamna Uba sani

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa wani Malamin Addini a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari cocin Katolika na Saint Raphael da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar.

A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindiga suka kona cocin inda aka kashe malamin Stephen Danlami.

Yayin da yake nuna fushinsa kan harin, Gwamna Sani a wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mohammed Shehu ya fitar, ya sha alwashin zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da tabbatar da cewa sun fuskanci fushin doka.

Gwamnan ya ce an kai harin ne da nufin haddasa rikicin kabilanci da na addini a jihar Kaduna da kuma zagon kasa ga kokarin gwamnati na sake gina rikon amana a tsakanin al’umma.

Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta binciki lamarin tare da tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata laifin tare da fuskantar fushin doka.

Ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa tare da ba su tabbacin gwamnatin jihar za ta tallafa musu a wannan mawuyacin lokaci.

Gwamna Sani ya bayyana cewa tun daga farko gwamnatin sa ta dauki kwararan matakai na maido da zaman lafiya a cikin al’ummomin da ke fama da rikici ta hanyar karfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro na tarayya tare da sake farfado da hukumar ta Kaduna (KADVS) ta hanyar daukar ma’aikata 7,000 da horas da ma’aikatan sa kai na Kaduna kwanan nan. KADVS).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button