Labarai

Ba zan taba gamsuwa da samun Natsuwa ba har sai an shawo kan rashin tsaro a Nageriya – Tinubu

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya ce ba zai gamsu ba har sai an kawar da rashin tsaro kwata-kwata daga kowane bangare na kasar nan.

A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, a Maiduguri.

Shugaban ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafi da kulawa ga iyalan dukkan ‘yan Nijeriya da suka yi fama da matsalar rashin tsaro a sassan jihar Borno.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button