Siyasa

Ba Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa A 2023 Ba, Mulki Kudu Zai Koma, Inji El-Rufa’i.

Spread the love

El-Rufai Yana Son Dan Kudu Ya Zama Shugaban Kasa A 2023

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce ba zai tsaya takarar shugabancin kasar nan 2023 ba.

A cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, El-Rufai ya ba da shawarar a mika madafun iko a 2023 zuwa kudanci kasar nan bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce: “Mutane da yawa suna ta cewa ina son yin takarar shugaban kasa tun lokacin da na ke Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT). “Wannan ba ma’ana. “Bana son [tsayawa takarar shugabancin Najeriya]. “Allah ne yake bada iko, ko kuna so ko basa so.

El-Rufai ya kara da cewa “Idan da Allah ya so, zai ba ka, amma ban yi niyyar yin takarar shugabancin Najeriya ba kuma wanda zai ce na yi.” El-Rufai ya kuma ce akwai yarjejeniya mai tsayi wacce idan arewa ta yi mulkin shekaru takwas, ya kamata a mika shugabancin kasar ga kudanci, tare da jaddada cewa duk da cewa ba a sanya yarjejeniyar a kundin tsarin mulki ba, amma ‘yan siyasa suna sane da hakan.

Gwamnan wanda yana wa’adin mulkinsa na biyu, ya ce: “Dalilin da ya sa na fito na ce bayan shekaru takwas da Shugaba Buhari, babu wani dan Arewa da zai yi takarar shugabancin kasa. “A bari mutanen Kudu su ma su samu shekara takwas.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button