Tsaro

Ba zan yarda da rikicin Kabilanci da Addini a Najeriya ba, zan kare dukkan addinai da kabilu — in ji Buhari.

Spread the love

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta kyale wata kabila ko wata kungiyar addini ta tada kiyayya da tashin hankali a kan wasu kungiyoyin ba.

A cewar shugaban a shafinsa na Twitter, gwamnatin Najeriya ta dukufa wajen tabbatar da tsaron dukkan ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.

Sakon ya biyo bayan rikicin kabilanci ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, biyo bayan zargin kisan wani Bayarabe da wani bahaushe mazaunin garin ya yi.

Arangamar ta haifar da tashin hankali, wanda ya yi sanadiyyar salwantar dukiya da kuma mutuwar wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba.

“Gwamnatinmu za ta kare dukkan addinai da kabilu a Najeriya, walau masu rinjaye ko marasa rinjaye, daidai da nauyin da ke wuyanmu a karkashin tsarin mulki. Ba za mu bari wasu kabilu ko kungiyoyin addini su nuna kiyayya da tashin hankali a kan wasu kungiyoyin ba, ”in ji Buhari.

“Ina kira ga shugabannin addinai da na gargajiya, da kuma Gwamnoni da sauran zababbun shugabannin a duk fadin kasa, da su hada kai da Gwamnatin Tarayya don tabbatar da cewa al’ummomin yankinsu ba su warwatse ta hanyar kabilanci da sauran matakan farko ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button