Labarai

Ba’a son raina Na taya ka murnar lashe zaben Gwamnan Edo ba, Buhari Ya Fada Obaseki

Spread the love

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, a ranar Juma’a, ya ce Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), cikin raha ya gaya masa cewa ba da son ransa ya taya shi murnar lashe zabensa ba saboda ya kayar da dan takarar jam’iyyarsa.
Gwamnan, wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party ya doke Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar All Progressives Congress na Buhari da sauran su don lashe zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a jihar Edo. Obaseki ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa a karshen ganawar da ya yi da Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce, “Mai girma Shugaban kasa, cikin halayyar sa ta barkwanci, ya ce ba son ransa ya taya ni murna saboda kayar da jam’iyyarsa. Ya kuma nuna cewa rawar da yake takawa, da farko a matsayinsa na Shugaban Najeriya, shi ne ya zama Shugaban kowa ba tare da la’akari da jam’iyya, kabila, ko akida ba. “Ba za mu iya neman karin bayani daga Mista Shugaban kasa ba, hakika ya taka mahimmiyar rawa a wannan zabe.


Obaseki ya ce shi da mukarraban sa sun kasance a Fadar Shugaban Kasa ne domin su gode wa Buhari kan dagewar da ya yi cewa dole ne a gudanar da zaben gwamna a jihar. Cikin Gaskiya “Saboda wannan aikin kadai, mun ji dole ne mu zo mu ce mun gode. Ba kawai ina zuwa tare da mataimakina ba ne, mun zo ne don in yi godiya tare da wakilan mutanen Edo – sanatocinmu, ’yan Majalisar Wakilai, manyanmu da shugabannin jam’iyyar,” inji shi. Obaseki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button