Babban Bankin Najeriya CBN ya karyata ikirarin rage darajar Naira, ya ce dala tana nan akan $1/N465.
Babban bankin ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin da wasu ke yi, domin hasashe ne da kuma aka ƙirƙire shi wajen haddasa firgici a kasuwa.
Babban bankin Najeriya CBN ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya rage darajar Naira zuwa kusan Naira 630 akan dala.
Tun da farko dai rahoton faduwar darajar kudin ne daya daga cikin jaridun kasar ta ruwaito.
Sai dai a wata sanarwa a ranar Alhamis, mukaddashin shugaban sashen sadarwa na bankin, Dr Isa Abdulmumin, ya bayyana hakan a matsayin karya.
“Rahoton labarai, wanda a tunanin jaridar ya keɓanta, cike yake da KARYA da ɓatanci, wanda ke nuna yiwuwar jahilci da gangan game da yadda kasuwar canji ta Najeriya ke aiki,” in ji shi.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, don kauce wa shakku, an sayar da farashin canji a kasuwar Investors’ & Exporters’ (I&E) a safiyar yau (1 ga Yuni, 2023) a kan Naira 465/US $1 kuma ya tsaya tsayin daka a daidai wannan farashin na wani lokaci.
Babban bankin ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin gaba dayansa, domin hasashe ne da kuma aka ƙirƙire shi don haddasa firgici a kasuwa.