Wasanni

Babban Burina Shine Na Zarce Messi Na Karya Tarihin Ronaldo A Fagen Kwallon Kafa, Inji Abdul Musa Zubairu.

Spread the love

Zamu tsaya tsayin daka don muga mun taimakawa ƙasarnan don muga ta sami nasarori a fagen ƙwallon ƙafa.

Ina so naga mun ciyowa Najeriya kofin Duniya, don muna ƙaunar kasarmu, kuma muna kishinta, don haka dole mu tsaya tsayin daka muga mun taimaketa.

Zan zama jakada na ƙwarai a duk inda naje wajen kare Darajar ƙasar mu tago Najeriya.

Yanzu muke kan ganiyarmu, kuma fatan mu kafa sabon tahiri a fagen ƙwallon ƙafa wadda zamu bawa duniya mamaki.

Bubban burina shine naga na zarce Messi na Karya tarihin Ronaldo a fagen tamola da yardar Allah, Inji Dan Wasa Abdul Musa Zubairu.

Abdul Musa Zubairu dai ɗan asalin Jihar kaduna ne, Yana da shekara 21 a yanzu haka.

Yayi wasa a ƙungiyoyi guda 4 kafin tafiyarsa
Nahiyar Turai (AS TRENCIN FC) A ƙasar Slovakia. (FORTUN LIGA) Itace gasa mai daraja ta ɗaya a ƙasar Slovakia.

Ƙungiyoyin daya buga wasa
1- Ogolos Fc
2- Bokaji Stars fc
3- Kaduna Bees fc
4- GBS ACADEMY
Suna Najariya ne duka.

A 2016 ya tafi Ƙarƙashin Jagorancin Kamfanin (KAS- CONSULTINING D.O.O) inda ya fara buga wasa a 2017 yana buga wasan tsakiya inda yake buga Lamba 10

A yanxu haka wasu ƙungiyoyi dake nahiyar turai na nemansa. Aciki Harda kulobɗin (Ajax)
Ƙasar Slovakia na kiran sa (N’gola Kante) sabida ƙwazon sa da nuna kishi a guri ƙwallo.

As Trencin na shiga damuwa idan babu shi a wasa.

Sunce Ɗan Wasan na da hazaƙa da kawo taimako don mu sami nasara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button