Babban Dan Jamal Khashoggi Ya Ce Sun Yafe Kisan Mahaifinsu.
Daga Haidar H Hasheem Kano
A jiya ne Salah Khashoggi babban dan Jamal Khashoggi, ya sanar da cewa sun yafe kisan mahaifinsu da jami’an tsaron kasar Saudiyya suka yi.
Tashar talabijin din gwamnatin Saudiyya ta bayar da rahoton cewa, Salah Khashoggi dan marigayi Jamal Khashoggi, ya sanar a shafinsa na twitter cewa; sun yi afuwa a kan wadanda suka yi wa mahaifinsu kisan gilla.
Sai dai a nata bangaren Agnès Callamard, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai harhada rahotonni kan cin zarafin bil adama a duniya ta bayyana cewa, tun farko sun yi zaton hakan, domin kuwa matsin lambar da iyalan Khashoggi suke fuskanta daga mahukuntan Saudiyya na nuni da cewa, daga karshe dai dole ne iyalan Khashoggi su saduda, matukar dai suna son rayuwarsu.
A karshen shekara ta 2018 ce dai wasu manyan jami’an tsaron masarautar Saudiyya, daga ciki har da masu tsaron lafiyar Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadon sarautar kasar, suka yi wa fitaccen dan jarida na kasar ta Saudiyya kisan gilla a cikin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Gwamnatin Amurka dai ta bayar da cikakkiyar kariya, tare da hana gudanar da duk wani bincike kan wannan lamari, musamman ma a kan Muhammad bin Salman, wanda shi ne babban wanda ake zargi da hannu wajen kashe Jamal Khashoggi, da ke sukar salon mulkinsa.