Labarai

Babban rashin hankali a nada Ganduje amatsayin Shugaban jam’iyar Apc ~Cewar mataimakin Shugaban APC na Kasa.

Spread the love

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa Salihu Lukman ya yi watsi da yunkurin nada tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya baiwa Mista Ganduje shawarar ya maye gurbin Abdullahi Adamu, bayan murabus din da ya yi a ranar Litinin.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Mista Lukman, wanda ya kasance babbar rundunar da ta yi kira ga Mista Adamu ya yi murabus, ya bayyana matakin a matsayin rashin hankali da kuma kashe kan jam’iyar

A cewar Mista Lukman, nadin Ganduje zai bata tsarin da jam’iyyar ta yi.

Gwamna Ganduje na fuskantar Bakin jinin siyasa tun bayan fitar bidiyon da aka hango gwamnan na karbar dalolin Amurka Yana cusawa a aljihun babbar Riga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button