Labarai

Babbar magana Kwamishinan ganduje yace ba karamin abun Haushi bane talaka Yayi zabe Kuma a kwace masa..

Spread the love

Tsohon Kwamishinan ganduje Win win Muaz Magaji ya caccaki na kusa da Buhari ya Kuma nuna bacin ransa Kan yadda talakawa sukayi zabe Kuma aka kwace masu inda yace dama in kaji ance kayi hakuri to an cuceka… Ka kara hakuri kuma to cutar da yawa…Talaka yayi zabe an kwace masa! wasu na ganin wannan habaici ne tsohon Kwamishinan yakeyima ganduje Kan Zaben sa da abba gida gida.

Har’ila yau Kwamishinan ya caccaki na kusa da shugaba Buhari inda yace Babu shasha shai marasa imani irin mutanenmu yan amshin shata dake tare da Buhari.. Yan abi yarima… Kiri kiri Buhari ya saki layin da aka zabeshi suna kallo ko uffan!

Daman can dai tsohon Kwamishinan yaron Engr Rabiu Kwankwaso ne idan Kuma baku manta ba shine Kwamishinan ayyukan ganduje Wanda aka cire bisa ga zargin murnar mutuwar Abba kyari…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button