Tsaro

Babbar Matsalar Da Gwamnatin Buhari Ta Samu Shine Bayyana Samun Nasara Akan Boko Haram Da Wuri, Inji Bulama Bukarti.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Shahararren lauya kuma me sharhi musamman akan harkokin da suka shafi kungiyar Boko Haram, Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewa kuskuren da gwamnatin Buhari ta yi shine bayyana nasara akan Boko Haram da wuri.

Ya bayyana hakane yayin da yake jawo hankalin mutane masu cewa akwai hannun gwamnati a cikin Boko Haram. Hutudole ya fahimci cewa Bulama yace a zamanin Mulkin Obasanjo Boko Haram ta fara kuma tun daga kan waccan gwamnati har zuwa yanzu akan danganta kungiyar da gwamnati.

Saidai a bayanin da yayi a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa baya zargi kowane shugaban kasa ko na kusa dashi da goyon bayan Boko Haram, Asalima a karkashin gwamnatin Buhari da wasu kewa kallon na sassautawa Kungiyar Boko Haram ta tafka asara da yawa inda aka kwace garuruwa da yawa daga hannunta sannan Gwamnatin Buhari ce ta yi nasarar kubutar da ‘yan Matan Chibok 100 daga hannun Boko Haram.

Bulama yace matsalar da Gwamnatin buhari ta samu shine ta bayyana nasara akan Boko Haram da wuri kuma yayin da kungiyar ta dawo, gwamnatin ta rika karyatawa har saida lamarin ya fara kazanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button