Labarai

Babbar Matsalata Da Kafa Yansandan Jihohi Shine Kada A Rika Amfani Da Makamai Ta Hanyar Da Bata Dace Ba~Shugaba Buhari.

Spread the love

Gwmamnatin tarayya ta bayyana cewa kalubalen dake tattare ds kafa ‘yansandan jihohi shine da yawan jihohin da suke kira a kafa ‘yansandan da wuya su iya biyan Albashi.

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a hirar da yayi da Channelstv inda yace shugaba Buhari na nuna damuwa cewa idan aka kafa ‘yansandan jihohin za’a iya amfani da makamai ta hanyar da bata dace ba.

Yace kuma jihohi da yawa dake maganar kafa ‘yansandan jihohi basa iya biyan Albashin ma’aikatansu yanzu haka. Yace to me kake tunanin zai faru idan kabar jami’in tsaro da makami a hannunshi tsawon watanni baka biyanshi Albashi ba?

Saisai ya karkare da cewa, gwamnatin na da shiri kafa ‘yansandan jihohin.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button