Siyasa
Babu Abin Da Buhari Zai Kara Tabukawa, Haka Zamuyi Ta Hakuri Dashi Har Ya Sauka, Inji Buba Galadima.

Daga Comr Yaseer Alhassan
Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa ba ya tsammanin shugaba Buhari zai gyara matsalolin dake gwamnatinsa, haka za’a ci gaba da hakuri dashi har ya sauka daga Mulki.
Buba Galadima yace har yanzu shi mutumin Buhari ne amma inda inda suka farraka tun da ya gane cewa shugaban kasar ya kaucewa tsarin da suka so a tafi akai.
Galadima da aka tambayeshin idan Buhari ya gyara matsalolin zai dawo su ci gaba da aiki tare?
Ya bayyanawa Sunnews cewa yafi su sanin Buhari dan haka ba zai gyara ba, haka za’a ci gaba da hakuri dashi har zuwa lokacin da zai sauka daga Mulkin.