Kungiyoyi

Babu abin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta tsinana mana sai ma ƙara mana yawan maƙiya da ta yi – Kungiyar Fulani Makiyaya, Miyetti Allah.

Spread the love

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana cewa babu abin da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta tsinana mata sai ma kara mata yawan makiya da ta yi.

Sakataren Kungiyar, Saleh Alhassan ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da Punch inda yace a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari an mayar da Fulani saniyar ware ana nuna musu banbanci.

Ya ce kuskurene a rika alakanta makiyaya da Shugaba Buhari saboda suma suna fuskantar wariya a zamanin Mulkinsa.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button