Labarai
Babu Aibu A Ciwo Bashi, Inji Lai Muhammad.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Ministan Sadarwa, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa babu wani aibu a ciwo bashi da wasu ke ta tada hankula akai.
Lai yace muddin bashi bawai an yi ayyukan yau da kullun dashi bane, indai ayyukan raya kasa ne aka yi to babu matsala dan an ciwo shi.
Lai Muhammad ya bayyana cewa bashin da suka ciwo daga kasar China da sauran kasashen Duniya sun yi amfani dashine wajen gina Titunan jirgin kasa da inganta wutar lantarki da sauransu.
Ya bayyana hakane yayin da yake duba ayyukan shimfida titin jirgin kasa a Ibadan. Ya jinjina bisa aikin da aka yi.