Tsaro

BABU ALAMAR KAREWAR TA’ADDANCIN A NAGERIYA

Spread the love

WAI KU GANI KUKEYI TA’ADDANCIN ZAI KARE DA SAURI A NAGERIYA HAKA?

Hmmm Kaso tamanin cikin darinmu na ”yan Nageriyarmu Azzalumai ne fadamun dan allah ta ina Za’a Kawo Karshen Ta’addancin?

Ta’addancin boko Haram Sun Mai dashi Kasuwanci idan an basu kudi domin sayen makamai sai su zuba kudin a bitalmanin aljihunsu..

Idan Ka Basu Kudi domin Inganta Ilimin Saisu inganta ilimin iyalansu dana ‘yan uwansu, babu ilimi dole talaka ya zama Babban dan ta’adda..

Idan ka basu kudi domin a inganta harkar noma sai su karkatar da kudin noman jiha State guda izuwa gidan gonarsu, Talaka babu abinci babu ilimi dole yayi sata ya zama dan garkuwa da mutane…

Kana Matsayin Shugaba idan ka kira malamai domin suyi maka wa’azi sai kwadayi yasa kawai su fada maka abin da ranka yakeso a maimakon su fada maka gaskiya dole shugaba ya zama azzalumi…

Idanmu matasa kuma mun Shiga Shafukan Sada Zuminci na zamani mun fada masu gaskiya saisu sa jami’an tsaro su kamemu a garkamemu a gidan yari…

Matsalar Ta’addancin zata kare ne kawai idan an kawo karshen wa’yan nan matsalolin maganar gaskiya kenan gwandama ku daina Yaudarar kanku da cewa za’a kawo karshen Ta’addancin domin masu kawo karshen Ta’addancin sune suke kasuwanci da Ta’addancin kunga kenan karewar Ta’addancin a Nageriya babu rana…

Ya allah Ya Kawo maku dauki Yaku Al’ummar sabon Birnin Jihar Sokoto..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button