Labarai

Babu Anfanin zama na a Majalisa idan har ba zan iya taimakon Al’ummar Arewa ba Inji Sanata Uba Sani

Spread the love

Sanata Uba sani Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya Shugaban Kwamitin bankuna Inshora da sauran harkokin kudi ya Tabbatar Mana da cewa Babu anfanin zamansa a Majalisar dattijan Nageriya matukar bazai iya taimakon Al’ummar da yake wakilta da jihar kaduna izuwa Arewacin Nageriya Baki daya ba
Sanatan yace ko da yaushe kokarin su a Majalisar dattijan shine ya za’ayi su gano hanyoyin da zasu kawo karshen Zaman Banza tare da kawo hanyoyin da zasu inganta harkar noma da harkar ililmi a Arewacin Nageriya musamman sassan dake fama da barazanar hare haren ta’addanci Wanda ke da nasaba da Rashin aikiyi, har’ila yau sanatan ya Kara Kira ga al’ummar Arewa cewa
Suyi anfani da damar su wajen taimakon ‘yan uwansu
Ma’ana duk wata dama da mutun yake da ita ya dubi Allah ya dubi Annabi s.a.w ya taimaki Arewa da ita domin ta Haka ne kawai za’a samu kwanciyar hankali da Arziki Mai dorewa a yankinmu na Arewa…

Matsayin sa na Shugaban Kwamitin bankuna a Majalisa yayi anfani da damarsa ya saka hannu ya wuce gaba gaba an karbo Bilyoyin kudi daga bakin lamuni na duniya duk domin taimakawa manoman Nageriya.

Sanata Uba sani kawo yanzu dai da zuwansa Majalisar dattijan Nageriya yayi aikin taimakon Al’ummar masu tarin yawa Amma ga wasu kadan daga aikin sanatan kamar Haka…

ILIMI Ya Kai kudri domin neman Samar da Makarantar FCE a karamar hukumar Giwa, tuni Shiri yayi nisa…

Kudirin Samar da asibitin gwamnatin tarayya a rigasa Shima shirinsa Yayi nisa yanzu…

Kokarin Samar da jami’ar tarayyar ta sanin kimiyyar daji dake Birnin Gwari

Kudrin Samun Izinin Chanja Polytechnic Makarantan kimiyya ta tarayya Zuwa jami’a a kaduna.

Ya gabatar da kudrin sanin ilmin na’ura Mai kwakwalwa (computer) da hanyar sadarwa ta zamani, duk domin taimakon matasa…

Ya dauki nauyin horar da matasa mutun dari 100 cikin mutun dubu 1,000 da yayi alkawari tare da kokarin sama masu jari Mai karfi daga babban bankin Nageriya CBN.

Sanata Uba sani yana yin ire iren Wa’yan Nan kokarin ne duk domin taimakon Al’ummar da yake wakilta izuwa Al’ummar Arewacin Nageriya Baki daya.

Zamu cigaba da bincike tare da kawo maku aikace aikecen wannan Sanata mai suna Malam Uba Sani ba don komai ba sai Don ya zama abin koyi ga sauran ‘yan Majalisar tarayyar nageriya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button