Ilimi

Babu gudu babu ja da baya akan ƙudirinmu na buɗe makarantu ranar Litinin mai zuwa, in ji Ganduje.

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bakin Kwamishinan Ilimin Jihar Kano Sunusi Sa’id Kiru ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano tana kan kudirinta na sake bude Makarantun Firamare da na Sakandire da ke Fadin Jihar Kano a ranar Litinin mai zuwa 18 ga Wannan watan Junairun da muke ciki.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai.

Da aka tambayeshi kan batun bude manyan makarantun gaba da Sikandiren dake fadin jihar, kwamishinan ya bayyana cewa ba shi da hurumi a wannan Bangaren.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button