Siyasa

‘Babu Sauran APC, Abinda Muke Da Shi Shine Girmama Buhari’ – Okorocha Yayi Raddi Ga Nasarar Obaseki.

Spread the love

Dan majalisar da ke wakiltar gundumar sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha, ya taya mutanen jihar Edo murna kan yaki da rashin adalci da aka ce an yi a zaben 19 ga Satumba.

An bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben.

Tsohon Gwamnan na Imo ya bayyana asarar da jam’iyyar APC ta yi a matsayin “juyin juya halin talakawa kan rashin adalci”.

Ya kuma bayyana cewa girmamawa ga shugaban kasa Muhamamadu Buhari shine duk abinda jam’iyyar ta bari.

Okorocha yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ya ce, “babu sauran APC, abin da muke da shi shi ne girmamawa ga Shugaba Muhammadu Buhari”.

Haka kuma Surukin Okorocha kuma tsohon dan takarar gwamna a jihar Imo a 2019, Uche Nwosu, ya zargi tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, da faduwar jam’iyyar, yana mai cewa “abin da kawai ya yi shi ne don kokarin rufe bakin mutane don kar su yarda dan takarar da ba su taba so ba ”.

“Wannan ba abin da aka gina APC a kai ba ne, muna sa ran za a yi abubuwa yadda ya kamata amma tsohon shugaban, Adams Oshiomhole, ya yi imanin cewa komai na iya zuwa daga ko’ina ba tare da bin tsarin da ya kamata ba,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button