Siyasa

Babu tsarin talaka a cikin tsarin Tinubu gashi yanzu burodi ya gagari talakawan Nageriya Akwai Yunwa a tsakanin Al’ummar Nageriya ~Atiku.

Spread the love

Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya koka da mulkin Tinubu inda Yake cewa A ‘yan makwanni ko nace watannin baya-bayan nan,’yan Najeriya a ciki da wajen kasar na ci gaba da cece-kuce kan yadda tattalin arzikin kasa ya shiga wani hali.’yan Najeriya na cikin damuwa mutuka Kuma suna da hujjar shiga damuwar, saboda rashin Kwarewar da Shugaba Tinubu ke nunawa wajen tunkarar kalubalen tattalin arzikin kasar na Kara tsawaita Nisan matsalar ta tattalin arziki.

Manufofin sa a wannan bangaren, da aka ɗora kan tsarin da suke kira na sabunta kyaƙƙyawan fata ga Najeriya, saɓanin haka Yana cirewa ‘yan Najeriya ragowar karfin gwiwar da suke da shi, ta hanyar ƙara haifar da raɗaɗi da rashin kwanciyar hankali. Bangarori masu zaman kan su na Kara shiga matsala, kananan ‘yan kasuwa na durkushewa yayin da manyan kamfononin kasa da kasa suka shiga rudani suna ficewa daga kasar.

Yanayin tsadar rayuwa a ƙauyuka da birane ya ƙara haifar da tsananin wahala da damuwa ga mutane. AKWAI YUNWA A TSAKANIN JAMA’A. Saboda abincin yau da kullum Kamar Burodi na neman fin karfin mafiya yawan ‘yan Najeriya.

Kasafin kuɗin sa na 2024 za a iya cewar Bata sauya-zani ba, saboda babu Ingantaccen tsarin yadda za a ɗauki matakan ɗora tattalin arzikin kasa kan tafarkin ci gaba. Saboda ya mayar da hankali ne kan abubuwa da zasu taimakawa tafiyar da Gwamnatin Tarayya, kasafin 2024 ba zai taimakawa tattalin arzikin kasa ba balle inganta rayuwar ‘yan kasa.

Shugaba Tinubu ya gaza nuna Kwarewa wajen tunkarar matsalolin da suke addabar ‘yan ƙasa da harkokin kasuwanci, bayan da aka cire tallafin man Fetur, da kuma sabon tsarin musayar kuɗaɗen waje.

Manufofin Shugaba Tinubu Babu talaka a cikin su, a bayyane take ya kasa kama bakin zaren, abubuwa sun Fi karfin sa.

Domin su lullube gazawar su, shugaba Tinubu da Mataimakan sa na Dora laifi a kan Wanda ya gabace shi cewa an Mika musu ruɓaɓɓen tattalin arziki. Wannan ba sabon abu bane, domin shi ma Shugaba Buhari yayi waɗannan kalamai lokacin da yake kan mulki. Kawai dai wannan na Kara jaddada abin da muka Sani, Tinubu ya Sami kan sa a shugabanci Bai Shirya ba.

Tinubu da tawagar sa kan tattalin arziki dole su amince da kura-kuran da suka tafka, da kuma gazawar su sannan su nemi taimakon waɗanda suka San kan abin. Wajibi ne su yi hakan cikin gaggawa kafin tattalin arzikin kasar ya nutse a tekun matsala.

Tambayar ita ce shin, zasu yi hakan? – AA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button