Addini
Babu Wanda ya isa ya kori bishop kuka daga jihar sokoto__Fadar shugaban kasa.
Shugaban kasar Najeriya muhammadu Buhari tabakin mai taimaka masa kan harkokin yada Labarai Malam garba Shehu, yace babu Wanda ya isa ya kori bishop kuka daga jihar sokoto.
Garba shehu yace abinda wata kungiya mai suna kungiyar hadin kan musulmi a jihar sokoto tayi bai dace ba, yasabawa dokar kasa.
Garba Shehu yace kira da kungiyar tayi wa shugaban wata coci ta jihar sokoto bishop kuka cewa koya janye kalaman Sa ko kuma yafita daga jihar sokoto ba daidai bane.
Garba Shehu yace bishop kuka Dan’ kasa ne yana “yan cin fadar albarkacin bakin Sa, kare addinin sa, yana da ikon shiga ko wanne gari ya zauna kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
Don haka wancan kira da wata kungiya tayi pastor bishop kuka bai dace ba.
Daga Kabiru Ado Muhd