Babu Wani Jinin Dan Najeriya Da Yake Buƙatar A Zubar Yayin Wata Zanga-zangar Lumana Ta Neman Ciyar Da Kasar Mu Gaba, Rokon Goodluck Jonathan Ga Masu Zanga-zanga.
Babu Wani Jinin Dan Najeriya Da Yake Buƙatar A Zubar Yayin Wata Zanga-zangar Lumana Ta Neman Ciyar Da Kasar Mu Gaba, Goodluck Jonathan yayi magana game da zanga-zangar #EndSARS
Tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya yi tsokaci kan zanga-zangar #EndSARS da aka gudanar a jihohi da dama a fadin kasarnan.
Tsohon Shugaban wanda ya bayyana cewa zanga-zangar na neman ciyar da Nijeriya gaba a matsayin wurin da kowa zai rayu da cikakken karfinsa, ya kara da cewa babu wani jini da yake bukatar zubewa.
Jonathan ya kuma roki kowa da kowa ya kame kansa.
Ya rubuta a shafinsa na Twitter; Babu wani jinin Najeriya da yake bukatar zubewa ko rasa rai yayin zanga-zangar lumana da ke neman ciyar da kasarmu gaba.
Wataƙila muna da ra’ayoyi mabanbanta game da al’amuran ƙasa, amma babu shakka yawancin mutane suna son abu ɗaya ne don Nijeriya: wurin da kowa zai rayu bisa cikakkiyar damar da ikon da Allah Ya ba mu.
Ina roƙon kowa ya kasance mai kamewa yayin da muke tafiya cikin waɗannan ƙalubalen.” In ji shi.