Labarai

Babu wani malami a Kano da zai iya mukabala da Sheikh Abdujabbar Domin duk Hadisan daya ambata Gaskiya ne dasu a Bukhari da Muslim ~Inji Dr Almuhajir

Spread the love

Dr Sheriff Almuhajir ya rubuta Kan Batun mukabala tsakanin malaman jihar Kano da da Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara Dr Yana Cewa A fahimta ta, matsalar Mallam Abduljabbar ita ce izgili da kuma amfani da kalamai ma su tunzurarwa, da kuma yunkurin bayyana galaba akan wasu kungiyoyin addini. Amma zancen muqabala tsakanin shi da gungun Malamai akan wannan maganar tamkar wasan kwaikwayo ne.

Domin dukkan hadisan da Abduljabbar ya karanto suna cikin Bukhari da Muslim, hakanan sharhar da yayi ba ta sabawa sharhar magabata ba. Har nake cewa, kila dai wasu sun shaafa ne da hadisan ko kuma ba su kai gare su ba. Amma tabbas babu wani Malami da zai yarda ya fito muqabala bayan ya san tabbas akwai hadisan da sharhohin su a littattafai ingantattu.

Yanzu dai tunda an iso turbar na tsira, to madallah. Ina bada shawara nan gaba 1) a rika shigar da hikimah wajen kalubalantar mutane 2) a daina taron dangi akan harkar ilimi domin faduwar dangi faduwar kungiya ne 3) a rika warware muhallin mas’alah kafin a shiga jidali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button