Labarai
Babu wata rashin Jituwa tsakanin Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima ~Cewar Fadar Shugaban Kasa.
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da ake yi na cewa shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima alaka ta yi tsami, inda ta bayyana hakan a matsayin karya daga ramin Yan wuta.
Har ila yau, ya ce a tarihin shugabancin Najeriya, babu wani mataimakin shugaban kasa da ya samu kwarin gwiwa da cikakken goyon bayan shugaban sa kamar Shettima.
Wadannan da dai sauransu na kunshe ne a cikin karramawar da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Stanley Nkwocha, ya yi na bikin cikar Sanata Shettima shekaru 58 da haihuwa.