Babu wata Tiriliyan daya 1tr da Gwamnatin Tinubu ta samu Sakamakon cire tallafin man fetir k@rya ne ~Cewar Shugaban kwadago NLC.
Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta karyata ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu na cewa an ceto Naira tiriliyan 1 tun bayan da gwamnatinsa ta daina biyan tallafin man fetur.
A wani jawabi da ya yi a fadin kasar a ranar Litinin, shugaban ya bayyana cewa an ceto jimillar Naira tiriliyan 1 tun lokacin da aka dakatar da biyan tallafin.
Da yake jawabi yayin zanga-zangar da kungiyar kwadagon ke ci gaba da yi a fadin kasar, Comrade Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, ya ce kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin tattaunawa da kungiyar kwadago ta bayyana cewa babu ko kobo daya da aka ceto.
Ajaero yayi magana ne a lokacin da shi tare da Festus Osifo na jam’iyyar Trade Union Congress (TUC) suka jagoranci masu zanga-zangar zuwa harabar majalisar dokokin kasar a ranar Laraba.
“Shugaban kasa ya yi magana game da N1trillion da aka ceto. Kwamitin da muka gana, sun shaida mana cewa kawo yanzu babu wani ko kobo da aka ceto.