Badakalar cin hanci da rashawa na Emefiele, Ganduje, Yahaya Bello na cikin jerin cin hanci da rashawa 100 da suka shahara a Najeriya


Kungiyar kare muhalli ta kasa (HEDA) ta sanya sunayen tsofaffin gwamnoni Abdullahi Ganduje da Yahaya Bello na Kogi da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele a cikin jerin laifuka 100 na cin hanci da rashawa a Najeriya.
HEDA ta bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai a ranar Litinin din nan karo na takwas na taron da aka yi kan kotun yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa da kuma cika manyan laifuka 100 na cin hanci da rashawa a Najeriya a Legas.
A ranar 11 ga Yuli, 2024, Mista Ganduje, na biyar a jerin sunayen, gwamnatin Kano ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da karbar cin hanci da ya hada da dala 413,000 da kuma Naira biliyan 1.38.
Ana zargin Mista Ganduje, matarsa Hafsat, dansa, Umar da wasu mutane shida da laifin karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila a shekarar 2016 da 2017 tare da hada baki wajen canza kudaden da aka tanada na kayayyakin kiwon lafiya tsakanin 2020 zuwa 2021.
Mista Bello, na 28 a jerin sunayen, yana fuskantar tuhumar karkatar da kudade da kuma karkatar da kudaden da suka kai Naira biliyan 80.2 da kuma Naira biliyan 10.
Har ila yau, a jerin sunayen da ake tuhuma na 27 na cin hanci da rashawa shi ne Mista Emefiele sakamakon dukiyar haramun da ta kai kimanin Naira biliyan 11.4.
Sauran wadanda suke a jerin sunayen manyan laifuka 100 na cin hanci da rashawa sun hada da Orji Uzor Kalu, kan badakalar kudi Naira biliyan 7.6, Ladi Adebutu, dan takarar jam’iyyar PDP a Ogun a zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga Maris, Ikedi Ohakim, bisa zargin karkatar da kudi Naira miliyan 270.
Shi ma tsohon Gwamna Willie Obiano mai badakalar kudi Naira biliyan 4 yana cikin jerin sunayen.
Shugaban kungiyar ta HEDA, Olanrewaju Suraju, ya ce taron an yi shi ne domin wayar da kan jama’a kan manyan laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya, inda ya ba da misali da muhimmancin fallasa masu aikata laifuka da kuma shigar da matasa cikin hakan.
Mista Suraju ya ce, “Na yi imanin cewa dole ne mu kasance masu fata a yakin da muke yi da cin hanci da rashawa, sannan kuma wayar da kan matasa a kan hakan zai taimaka matuka wajen inganta al’amura.
“Kamar yadda za ku iya lura, yin hakan akai-akai zai zama izina ga masu aikata wadannan ayyukan lalata da kuma haifar da tsoro a tsakanin wasu da ke da niyyar yin hakan.”
Shugabar taron, Funmi Falana, ta yi nuni da cewa akwai bukatar a sanya ido kan yadda kasarnan ke fitar da cin hanci da rashawa da kuma wadanda suke karba.
“Idan babu mai karba, wanda zai bayar zai yi jinkirin bayarwa. Ba wai kawai ana maganar yadda ake kwashe kuɗinmu ba. Muna kuma son ganin yadda za a maido mana da kudaden da aka kwashe daga kasar da aka kai su,” in ji Ms Falana.
HEDA ta shirya shirin ne tare da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur.