Bai kamata ku dauki siyasa a matsayin yaki ba, Jonathan ya gargadi ‘yan siyasa.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya roki ‘yan siyasa da kada su dauki siyasa kamar yaki a yayin zaben shugaba.
Jonathan ya fadi haka ne a Yenagoa yayin taron godiya da gwamnatin Bayelsa ta shirya don bikin zagayowar ranar farko ta Douye Diri, gwamnan, a ofis.
Jonathan ya nemi ‘yan siyasa da su inganta zaman lafiya, kauna don kwanciyar hankali da ci gaban kasa, ya kara da cewa bayan zabe, ya kamata a samu hadin kai a tsakanin dukkan jam’iyyun siyasa.
Tsohon shugaban kasar ya ce bayan duk wani tsari na siyasa, ya kamata kowa ya zo ya ba da goyon baya ga wanda Allah ya so ya kasance a wurin.
Ya yaba wa Diri saboda “bude hannayensa” ga sauran jam’iyyun siyasa a jihar, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
“Nan da nan ka ci zabe kai tsaye ka zama gwamnan kowa ba tare da nuna banbancin jam’iyya ba,” in ji shi.
“Babu wani abu ne mara kyau ba gwamna ko shugaban kasa ya zabi wani daga wata jam’iyyar siyasa ya sanya shi ko Minista ko Kwamishina.”
A cikin jawabinsa, Diri ya yabawa bangaren shari’a da kuma kotun koli, musamman kan tabbatar da zaben nasa, yana mai cewa ma’aikatar tana ci gaba da kasancewa begen talaka.
Gwamnan ya kuma yi kira ga wadanda suka bar Jam’iyyar PDP zuwa wasu jam’iyyun siyasa da su dawo saboda jam’iyyar “ta isa ta saukar da su”.