Labarai
Ba’kin da APC ta shigo dasu A Gabanin Zaben 2019 Sune suka Addabi nijeriya da ta’addanci. A cewar jam’iyyar hamayya Ta PDP
Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta nuna rashin Jin dadinta game da yadda harkar tsaro yake tabarbarewar Akasar nan musamman A jahohin borno, Katsina, zamfara,sokoto da kogi da taraba
PDP tace rashin tsaro a wadanan jahohi da wasu sasssa na nijeriya gazawar Gwabnatin APC ne
Sanan tayi zargin ba’kin hauren da APC tayi amfani dasu a zaben 2019 wadanda ta debosu daga nijar da chadi da kamaru sune suka rikede suka koma ‘yan ta’addah
PDP tayi Kira da buhari da yatashi daga dogon barcin da yake yakawo karshen hare haren Yan ta’addah a nijeriya A cewar jamiyyar hamayya ta PDP ta bakin sakataren watsa labaran ta Kola olabandiyang