Siyasa

Bamu Da Hannu A Gayyatar Da DSS Tayiwa Ghali Na’Abba, ‘Yan Siyasa Na Gaske Kadai Muke Kulawa, Cewar Fadar shugaban kasa.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Fadar shugaban kasa ta yi magana akan yanda ake danganta kalaman da tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na’abba yayi akan gwamnati da gayyatar da DSS ta masa.

Da yake magana da manema labarai a jiya, Lahadi, me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, babu alaka tsakanin gayyatar da DSS tawa Ghali Na’abba da kalaman da yayi akan gwamnati. Mun fahimci Garba yace ‘yan Siyasa na gaske ne idan suka yi magana take daukar hankalin gwamnati kuma ta mayar da martani.

Yace amma maganar da Ghali na’abba yayi bata dauki hankalin gwamnatin ba dama sauran ‘yan siyasa na gaske. Mun ruwaito Garba na cewa ‘yan Siyasa masu kokarin daukar hankalin mutane basa damun Gwamnati.

Ya baiwa na’abba shawarar ya daina alakanta Gwamnati da gayyatar da DSS ta masa yaje ya ji da abinda ya jawowa kansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button