Siyasa

Bamu Soke Tsare – Tsaren Da Aka Gudanar Lokacin Marigayi Abba Kyari ba — Fadar Shugaban Kasa

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ta Musanta Labarin Da yake Zagayawa a Kafafen Sada Zumunta, Da yake Bayyana Cewar Gwamnatin Tarayya Ta Soke Dukkannin wasu Tsare – Tsare Da Ganawar Da Ta shirya Gudanarwa Lokacin Da Marigayi Malam Abba Kyari yake da Rai kuma yake a Matsayin Sakatare, Wato Magatakardar Fadar Shugaban Kasa, Inda Labarin yake Bayyana Cewar An Sabunta Jadawalin Da Sababbin Tsare – Tsare Da kuma Ganawa, Biyo Bayan Darewar Farfesa Gambari Kujerar Ta Marigayi Malam Abba Kyari.

A Takaitaccen Jawabin Da ya Wallafa a Shafinsa Na Twitter, Mai Magana Da yawun Fadar Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, ya Bayyana Cewar Kwata – kwata Babu Kamshin Gaskiya a Cikin Labarin, Inda ya Bayyana Cewar Babu Wani Jadawali Da Aka Canza Biyo Bayan Nada Gambari a Matsayin Sakataren Fadar Ta Shugaban Kasa, Inda ya Bukaci Al’umma Da Suyi Watsi Da Labaran Domin kuwa Labarai ne Na Shifcin Gizo Ko Ince Kanzon Kurege.

Idan Baku Mantaba ba Dai Abba Kyari ya Kasance a Matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya tun a Wa’adin Mulkin Shugaba Buhari Na Farar Hula Na Farko, wato daga Shekarar 2015 Zuwa Shekarar 2019, Inda Daga Bisani Bayan Darewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Kujerar Mulkin Kasarnan a Karo Na Biyu a Shekarar 2019 ya sake Nada Marigayi Abba Kyarin a Matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya a Karo Na Biyu, Kafin Allah yakarbi Ransa a Sanadiyyar Wannan Annoba Ta Covid – 19 a Shekarar nan damuke Ciki Ta 2020,

Bayan Rasuwar Ta Abba Kyari ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Amince Da Nada Farfesa Ibrahim Gambari a Matsayin Sabon Sakataren Gwamnatin Ta Tarayya, Kafin Nadashi a Wannan Mukami Na Sakataren Gwamnatin Tarayya a Wannan Shekarar Ta 2020, Farfesa Gambari Dai ya Kasance Tsohon Minista ne a Wa’adin Mulkin Shugaba Buhari Na Soja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button