Labarai

Ban bayyana Naira tiriliyan 9 a matasyalin dukiyar da na mallaka ba – Gwamnan Zamfara Dauda Lawal

Spread the love

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce bai bayyana tsabar kudi da jari, da kadarorin Naira tiriliyan 9 ba.

Lawal ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da Rediyon Faransa RFI Hausa.

Ya ce al’ummar Zamfara ba za su fuskanci kalubale mai yawa ba idan yana da Naira tiriliyan 9, ya ce da ya yi amfani da kudin wajen ci gaban jihar.

Gwamnan ya ce wannan zargin hasashe ne da mutane ke neman haddasa barna, inda ya ce kadarorinsa na nan ga masu son tantancewa.

“Ina fata haka kuma ina rokon Allah Ya ba ni irin wannan kudin. Allah Ya ba ni irin wannan kudi domin in taimaki jama’ata,” inji shi.

“Idan ina da irin wannan kudi, duk kalubalen da mutanena ke fama da su, da na yi amfani da kudin wajen magance matsalolin.

“Yanzu wannan batu na jama’a ne kuma akwai fom ga wanda yake so ya tabbatar ya zo ya yi.

“Wannan ba komai ba ne illa zargin da ‘yan barna ke yi, wadanda suke son ja da sunana a cikin laka amma na gode wa Allah, a kan wannan kudi da suke zargin na ayyana, ina rokon Allah Ya ba ni makudan kudi don haka. Zan iya amfani da shi don taimakawa mutane na. “

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button